Tsohon shugaban kasar Benin, Mathieu Kerekou wanda ya yi fice wurin jaddada dimokradiyya a nahiyar Afrika, ya rasu yana da shekaru 82.
Mista Kerekou ya hau karagar mulki tun shekarar 1972, inda ya yi mulkin kasar sau biyu a shekaru kusan 30.
Daga bisani bayan ya amince da dimokradiyya, wacce ta tanadi tsarin jam'iyyoyi da dama, sai ya sha kaye a zaben shekara 1991.
Tsohon shugaban, shi ne na farko cikin shugabannin Afrika da ya amince da kayen da ya sha a zabe.
Shugaban kasar na yanzu Thomas Boni Yayi, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kwar jini, kuma ya bayar da mako guda a kasar domin alhinin rashin.
Title :
Tsohon Shugaban Benin Kerekou ya rasu
Description : Tsohon shugaban kasar Benin, Mathieu Kerekou wanda ya yi fice wurin jaddada dimokradiyya a nahiyar Afrika, ya rasu yana da shekaru 82. Mist...
Rating :
5