Gwamnan farar hula na farko a jihar Bayelsa, Diepreye
Alamieyeseigha yua rasu bayan wata doguwar suma da
ya yi a asibiti a ranar Asabar.
Tsohon gwamnan ya rasu ya na da shekaru 63 a duniya.
Gwamnan jihar Dr. Ifeanyi Okowa ya bayyana marigayin
da cewa wani babban jigo ne a siyasar jihar wanda
mutuwarsa wata babbar rashi ne.
Yayin da danginsa kuma suka bayyana shi da cewa wani
gagarumin shugaba ne wanda mutuwarsa ta girgiza su
matuka.
A farkon makon nan ne gwamnatin Britaniya ta nuna
aniyarta ta a mayar da tsohon gwamnan kasar domin
amsa tuhumar da ake yi masa na halarta kudin haram.
An dai taba kama marigayin a watan satumba 2005 a
London ne aka kuma gurfanar da shi a gaban kotu a bisa
laifin halarta kudin haram, amma da aka bayar da belinsa
sai ya tsere a bayan ya yi shigar mace, a inda ya gudo
Najeriya, zargin da ya karyata.
Title :
Tsohon Gwamnan Bayelsa ya rasu
Description : Gwamnan farar hula na farko a jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha yua rasu bayan wata doguwar suma da ya yi a asibiti a ranar Asabar. ...
Rating :
5