Cikin daren jiya wasu tagwayen bamabamai suka
tashi a wani masallaci dake anuguwar Malai a
Maidugurin jihar Borno.
Anguwar Malai tana dap da
shiga birnin Maiduguri ne nan bamabaman suka
tashi suka kuma yi sanadiyar mutuwar mutane da
dama da kuma raunata wasu.
Tashin bamabaman ya zo ne bayan kwana biyu da
aka samu tashin wasu bamabaman a anguwar
Sajeri da suka hallaka rayukan mutane hudu da
kuma raunata guda goma sha uku.
Cikin 'yan kwanakin nan al'ummar birnin
Maiduguri na cigaba da fuskantar matsalar hare-
haren bamabamai sanadiya kutsawa cikin jama'a
da 'yan kunar bakin wake ke yi.
Amma bam din da ya tashi a anguwar Malai ana
kyautata zaton an boyeshi ne kana aka tada shi a
daidai lokacin da ake sallar magaruba.
Wani ganao ya shaidawa Muryar Amurka cewa
wadanda suka mutu zasu kai kamar mutane goma
banda wadanda suka ji rauni. Bam na farko da ya
tashi ya sa masallacin ya rushe kan mutane. Ana
kokarin taimaka masu kuma sai na biyun ya tashi.
Da alamu 'yan Boko Haram suna sake kama suna
shiga jama'a suna aikata ta'adanci. Ko a Gwozah
shekaranjiya wasu da ake kyautata zaton 'yan
kungiyar Boko Haram ne sun shiga garin sun yiwa
wasu mutane tara yankan rago.