Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce sojojinta sun
kashe mafi yawancin daga cikin mayakan Boko Haram da
suka kutsa cikin garin Gaidan na jahar Yobe da
yammacin ranar Laraba.
Sai dai kuma wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta
rasa sojojinta uku a lokacin musayar wutar da suka yi da
mayakan na Boko Haram.
Rahotannin farko-farko dai sun ce mayakan na Boko
Haram sun ci karfin sojojin a arangamar da suka yi a
garin, abin da ya ba su damar rike garin har na tsawon
dare.
Lamarin da kuma ya mayakan Boko Haram suka fasa
wasu shaguna domin kwasar ganima .
Title :
Sojoji sun kashe 'yan Boko haram a Gaidam
Description : Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce sojojinta sun kashe mafi yawancin daga cikin mayakan Boko Haram da suka kutsa cikin garin Gaidan na ...
Rating :
5