Rundunar sojin Isra'ila ta fara aikawa da daruruwan
dakarunta zuwa birane daban-daban na kasar domin
taimaka wa 'yan sanda su murkushe Palasdinawan da ke
kai hare-haren bidigogi da wukake a 'yan kwanakin nan.
A gabashin birnin Kudus, an bayar da umarnin kafa
wuraren binciken abubuwan hawa, ko da ya ke ba a kafa
su a yankunan Palasdinawa ba, inda ake samun
yawancin hare-haren.
An fara daukar matakin ne sakamakon amincewar da
gwamnati ta yi ta bai wa 'yan sanda damar rufe wasu
yankuna na gabashin birnin Kudus.
Kazalika, hukumomin na da damar rushe gidajen
Falasdinawan da ke kai hare-hare a kan Yahudawa,
sannan a hana su 'yancin ci gaba da zama a birnin
Kudus.
An ci gaba da rikice-rikice a yankin ne sakamakon kwana
da kwanakin da aka kwashe ana zaman zulumi a kan
samun damar shiga Masallacin Al-Aqsa mai muhimmanci
da Musulmai da Yahudawa.
Title :
Sojin Isra'ila na shirin tunkarar Falasdinawa
Description : Rundunar sojin Isra'ila ta fara aikawa da daruruwan dakarunta zuwa birane daban-daban na kasar domin taimaka wa 'yan sanda su murk...
Rating :
5