shugaban Amurka Barack Obama ya
umarci gwamnatin Amurka da ta fara shirin
dagewa Iran takunkuman da aka kakaba mata.
Bisa abinda aka kira da ranar
fara zartar da yarjejeniyar Nukiliyar Iran din da
kasashen 6 masu fada aji suka kulla a watan Yulin
da ya gabata.
Wannan fara shirin ne zai zama matakin farko na
yin aikinda yarjejeniyar kamar yadda aka kullata.
Obama ya fada a jiya Lahadin cewa,
“na yi maraba da wannan muhimmin matakin ci
gaba, sannan mu da abokan huldarmu dole mu
fuskanci mataki mai wahala na aiwatar da
yarjejeniyar da ta hadamu game da shirin
Nukiliyar Iran.”
Don tabbatar da cewa ba za a iya kera Nukiliya a
wajen ba Kungiyar Tarayyar Turai ma ta mika
kundin wa membobinta damar dubawa da kuma
tsaida takunkuman.
A wata sanarwa a talbijin Iran din ta bayyana
cewa, kasar zata cika sharuddanta, sannan ko a
makon da ya gabata jami’an Iran sun ce, nan da
karshen shekarar nan za su gama cika nasu
ka’idodij.
Title :
Shugaban Amurka Ya Bukaci Kasar
ta Soma Shirin Cirewa Iran
Takunkumi
Description : shugaban Amurka Barack Obama ya umarci gwamnatin Amurka da ta fara shirin dagewa Iran takunkuman da aka kakaba mata. Bisa abinda aka kira...
Rating :
5