Makon yija ne sabon shugaban hukumar kwastan
Kanar Hamidu Ali mai ritaya ya sanarda da cire
shinkafa daga jerin kayan abinci da gwamnatin
tarayya ta hana shigo dasu.
Matakin da Kanar Ali ya
dauka yanzu ya amince da shigowa da shinkafa
kasar daga kasashen waje.
Wannan matakin bai yiwa 'yan majalisar wakilan
Najeriya dadi ba. Onarebul Ibrahim Usman Auyo
dake wakiltar mazabar Hadeija da Auyo da Kafin
Hausa a majalisar tarayyar Najeriya yace matakin
koma baya ne ga manoma shinkafa cikin Najeriya
kuma ba zai haifar da da mai ido ba ga talakan
kasa..
Yace Hadeija-Jama'are ta shafi kusan jihohi hudu
duk suna noman shinkafa. Yace rashin inganta
aikin noman shinkafa da ingantata ya sa
manoman basa samun riba. Yanzu kuma da za'a
kwararota daga waje ke nan an karya manomanta.
Indan gwamnatin tarayya ta inganta noman
shinkafa Najeriya zata ciyar da kanta da sauran
kasashen dake makwaftaka da ita.
Shi ma Onarebul Rabiu Garba Kaugama daga jihar
Jigawa cewa ya yi Kanar Hamidu Ali ya wuce gona
da iri domin dokar hana shigo da shinkafa daga
kasashen waje doka ce ta majalisar tarayya.
Kamata ya yi ya tuntubi majalisar. Mutum daya ba
zai iya ture dokar majalisa ba. Majalisar ta
aiwatar da dokar ce saboda inganta manomanta
da kuma kare kawo wasu cututuka kasar. Matakin
da shugaban hukumar kwastan ya dauka na
gurgunta manoman kasar ne.