An bayyana wannan ne a taro na 21 na National Economic Summit, a jiya a Abuja. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ne a madadin yan uwan shi gwamnoni yayi rokon inda ya bayyana cewa satar shanu batun wasa da tsaron yankin. Yace:
“Munyi kokari mu samu taimako daga gwamnatin tarayya amma abun bai yiyu ba domin gwamnati bata da kudi. Amma wani hadin gwiwa da gwamnonin yankin suka yi ya rage aikin yan ta’addan inda aka maido da shanu 12,000.”
El Rufai ya bayyana cewa gwamnonin yankin sun hada wata runduna domin dalili aikin yan ta’addan a yankin. Akan sha’anin ilimi kuma, gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar a samar fida malami. Domin ki man in kashi 60 na malaman basu dace da karantarwa ba. Ana bukatar malaman lissafi da na turanci 3000.
Title :
Satar Shanu: Gwamnonin Arewa Sun Roki Shugaban Kasa
Description : An bayyana wannan ne a taro na 21 na National Economic Summit, a jiya a Abuja. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ne a madadin yan uw...
Rating :
5