A Najeriya, Majalisar dattawan kasar ta fara zama domin tantance mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata domin nadawa a matsayin ministoci.
Da safiyar Talata ne dai 'yan Majalisar ta dattawa suka hallara a zauren majalisar, kuma suna can suna yin muhawara domin fito da hanyoyin da za su bullowa batun tantance ministocin.
Tuni dai wasu daga cikin mutanen da aka mika wa majalisar sunayensu suka fara isa harabar majalisar.
Wasu daga cikin su su ne: Audu Ogbeh, Amina Mohammed.
Shugaban Majalisar ya ce za su tantance mutane goma ranar Talata, cikin su har da Amina Mohammed, Sanata Udo Udoma, Dr Kayode Fayemi, Chief Audu Ogbe, Dr Ogbonnaya Onu.
Kazalika, wasu shugabannin jam'iyyar APC mai mulkin kasar suna can a harabar majalisar ta dattawa, cikin su har da shugaban ta, John Odigie-Oyegun.
A makon jiya ne dai shugaban Nigeria ya aika da sunayen mutane 21 -- cikin su har da tsoffin gwamnonin jihohi da manyan 'yan siyasa.
Haka kuma, shugaban ya aika da karin sunayen mutane goma sha biyar ranar Litinin ga Majalisar ta dattawa domin tantancewa, kuma ana sa ran shugaban majaliasar, Bukola Saraki zai bayyana sunayen su.
Title :
Sanatoci na tantance ministocin Nigeria
Description : A Najeriya, Majalisar dattawan kasar ta fara zama domin tantance mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata domin nadawa a matsayin...
Rating :
5