Hukumar 'yan gudun hijira ta duniya IOM, ta ce ana
samun karuwar yara da mata da ake safararsu daga
Najeriya zuwa Italilya a wannan shekarar.
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce kimanin yara
da manyan mata 4,371 ne suka isa Italiya ta ruwa tun
daga watan Janairu.
Sanarwar ta ce kashi 80 cikin 100 na wadannan mata an
yi safararsu ne, kuma yawancinsu daga jihar Edo da ke
kudancin Najeriya.
Hukumar ta yi kira ga Italiya da ta yi gaggawar samar da
wani mataki na taimakawa wadannan matra da kuma
hana safararsu.
A kan azabtar da irin wadannan mata da aka yi safarasu
ta hanyar dukansu ko yi musu fyade a yayin da suke
tafiyar , kuma ana mayar da su tamkar bayi a Italiya da
sauran kasashen Turai.