A karon farko ya hado kan dukkan sarakuna
gargajiya dake kananan hukumomin Barikin Ladi
A ci gaba da neman
hanyoyin zaman lafiya a tsakanin al’umomin dake
gabada juna a jahar Filato, kwamitin da majalisar
dokokin jahar ta kafa dan gano musabbabin
rikicin da bada shawarwari kan matakan da za’a
dauka.
A karon farko ya hado kan dukkan sarakuna
gargajiya dake kananan hukumomin Barikin
Ladi,da wasu bangaren Mangu da jami’an tsaro.
A zaman tattaunawar da sukayi dukkani
al’umomin sun bayyana rashin jindadin su da
taske tashen hankulan dake kai rasa dinbin rayuka
da dukiyoyi.
Dagwon Rei, na Barikin Ladi Edward Buot, ya ce
irin wannan taron nada mahimmanci domin inda
kowa yayi maga daga nan sa’a gano bakin zaren
har a samun mafitar babu wanda bai son a zauna
lafiya da Fulani kamar yadda ake da can.
Shima Umaru Baba, Ardon, Langai daga karamar
hukumar Mangu, ya bayyana cewa barin kowa ya
koma wurin san a assali zai taimaka wajen samun
zaman lafiya.
Kwamandan rundunar tabbatar da tsaro a jahar
Filato, Brigediya Janar M H Madaki, ya bukaci
al’umomin ne dasu dunga fadin gaskiya dan yiwa
kansu adalci, ya ce rundunar tsaro da STF, ba zata
yi amfani da karfi wajen kawo zaman lafiya ba sai
in ku jama’a ku rugumi zaman lafiyar da kan ku.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin
majalisar dokokin jahar Filato Yusuf Adamu
Gardi, ya ce kamata yayi Gwamnatin tarayya ta
karo jami’an tsaro kamar yadda tayi a arewa
maso gabashin Najeriya.