Rundunar Sojin Nigeria ta gargadi Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya ta sake yin gargadi ga mayakan
Boko Haram da su gaggauta mika wuya kafin dakarun
sojin kasar su murkushe su.
Sanarwar gargadin mai lakabi 'gargadi karo na biyu'
Kanar Sani Usman Kuka Sheka kakakin rundunar Sojin
kasar ne ya sa hannu.
Sanarwar gargadin ta bukaci duk wani ko wa su 'yan
kasar da ke da alaka da mayakan Boko Haram da su
gaggauta ba su shawarar ajiye makaman su kafin lokaci
ya kure musu.
Sannan ta ci gaba da cewa rundunar ta gano
sansanoninsu da sauran in da su ke boye kuma a shirye
ta ke da ta murkushe su idan har ba su mika wuya ba.
Wasu mayakan kungiyar Boko Haram 200 ne su ka mika
wuya a Geidam a kwanakin baya.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a ranar Lahadi
ta ce ta fatattaki 'yan Boko Haram a Nafari da Gonin
Kurmi a inda 'yan kungiyar suka gudu zuwa dajin
Sambisa
Kungiyar Boko Haram ta zazafafa kai hare-hare a Najeriya
duk da ikirarin nasarar da rundunar sojojijn ta ke yi na
samun galaba akan su.