Rundunar hadin gwiwa ta kungiyar tarayyar Afrika (AFS)
ta soma gudanar da atisaye a filin motsa jini na Afrika
na Kudu.
Rundunar, wacce aka yi wa lakabi da 'Amani Afrika' tana
son tabbatar da cewa dakarunta na African Standby
Force (ASF), za su zamo a shirye domin gudanar da aiki
zuwa karshen shekara.
Bayan motsa jinin, ana kyautata zaton rundunar wacce ta
tanadi sojoji 25,000, za su fara kai daukin gaggawa ga
kasashe masu bukata a nahiyar Afrika.
An shirya wannan atisayen ne da tsarin shirin kwaikwayo
na yadda za su gudanar da dauki ga wata kasa da ta
shiga tarzoma.
Daya daga cikin dalilan da ya sa aka kafa ASF shi ne
domin kaucewa yawan neman sa hannun kasashen waje
domin kawo dauki ga duk wani tashin hankali a Afrika