Dan wasan Real Madrid Christiano Ronaldo ya kafa tarihi bayan ya zura kwallaye biyu a wasan da suka fafata da Malmo a ranar laraba a gasar cin kofin zakarun turai, lamarin da ya bashi damar kamo Raul a matsayin wanda ya fi ci wa Kungiyar kwallaye a tarihi.
An jima da zura idanu domin ganin ranar da Ronaldo zai kamo Raul wanda ya ci wa Real Madrid kwallaye 323 a cikin wasannin 741 da ya buga mata tsakanin shekara ta 1994 zuwa shekaraa ta 2010 kuma a yanzu sun yi kunnan doki.
A jumulce dai, Ronaldo ya zura kwallaye 500 cif cif a wasanni 753 da ya yi wa Real Madrid da kuma Kasarsa, Portugal.
Har ila yau, Ronaldo shine wanda ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai, inda ya ke da kwallaye 82 yayin da Lionel Messi ke biye da shi da kwallaye 77.