Akalla mutane hudu aka kashe a babban birnin
Brazzaville na kasar Congo, a lokacin wata zanga zangar
da aka yi kan shirye shiryen da shugaban kasar yake na
tsayawa takara a karo na uku.
An ce 'yan sanda sun yi harbi kan masu goyon bayan
'yan adawa a kewayen kudancin babban birnin, yayin da
mutanen suka yi kokarin dannawa cikin tsakiyar birnin.
An kone ofisoshin 'yan sanda da kuma motoci, sannan
mutane na tserewa daga yankin da kayayyakinsu.
Kakakin gwamnati dai ya musanta cewa akwai wanda ya
mutu, sannan ya ce lamarin bai kai ya kawo ba.
An dai katse harkokin sadarwa na intanet da sakonnin
waya, sannan an rufe hanyoyin da za a iya sauraron
gidan redion Faransa.
Title :
Rikici ya barke a Congo
Description : Akalla mutane hudu aka kashe a babban birnin Brazzaville na kasar Congo, a lokacin wata zanga zangar da aka yi kan shirye shiryen da shuga...
Rating :
5