Wata rigima ta kunno kai tsakanin wasu 'yan
gudun hijira daka garin Baga dake karamar
hukumar Kukawa da gwamnatin jihar Borno
Rigimar ta samo asali ne
domin gwamnatin jihar tace ita bata san da
zamansu ba.
Kwanaki biyu da suka gabata 'yan gudun hijiran
suka shiga garin Maiduguri daga Baga sakamakon
yunwa da suka ce suna fama da ita a garin tun
lokacin da suka koma. Mutanen sun koma Bagan
ne lokacin da rundunar sojin Najeriya ta sake
kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram amma
ba da sanin gwamnati ba.
'Yan gudun hijiran sun zargi gwamnati da cewa
tun lokacin da suka koma Baga gwamnati bata
ziyarcesu ba ko ta aika wani ya ga halin da suke
ciki. Bugu da kari sun yi zargin cewa sojojin dake
garin suna hana shiga ko fitar da abinci. Ban da
haka wai sojojin sun hanasu yin sana'arsu ta
kamun kifi ko yin noma. Sun ce lamarin ya jefasu
cikin halin kakanikayi.
Malam Bunu Abatcha daya daga cikin 'yan gudun
hijiran da suka shiga Maiduguri daga Baga yace
yunwa ce ta korosu. Abinci ya yi wani mugun
tsada a Bagan. Kwanun shinkafa guda daya nera
2,500 ne. Kwalbar fanta nera 250 take.
Musa Alhaji Bukar Kukawa shugaban karamar
hukumar Kukawa ya karyata zargin rashin kulawa
da 'yan gudun hijiran. Komawar 'yan gudun
hijiran Baga ba da sanin gwamnatin jihar ba ne.
Saboda haka ne sojoji suka hanasu kamun kifi ko
yin noma. Wadanda suke sansanin 'yan gudun
hijira da gwamnati take sane dasu ana basu
abinci.
To saidai shugaban hukumar bada agajin gaggawa
Injiniya Satome Ahmed yace mutanen dake
ikirarin sun fito daga garin Baga basu sanar dasu
a hukumance ba. Da suka shiga Maiduguri basu
gabatar da kansu ga hukumar dake kula da 'yan
gudun hijira ba. Maimakon haka sai suka hada
baki da wasu 'yanuwansu dake cikin sansanin suka
shiga. Saboda haka hukuma ta shiga ta ciresu daga
sansanin domin ba'a sansu ba.
Yanzu dai an hadasu da jami'an tsaro su
tantancesu. Idan basu da matsala gwamnati zata
san abun da zata yi dasu.