Farfasa Muhammad Al'Amin shugaban hukumar
samarda gidaje dake Abuja yace rayuwar 'ayn
gudun hijira dake tsugune a sansanoni daban
daban na cikin mawuyacin hali.
Shugaban hukumar ya
bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci jihar
Borno saboda gani da idanunsa halin da 'yan
gudun hijiran ke ciki.
Farfsa Al'Amin ya kwana a daya daga cikin
sansanonin 'yan gudun hijiran inda suke tsugune
cikin garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.
Farfasa Al'Amin yace ya ji ya kuma gani irin
yadda 'yan gudun hijiran ke gudanar da
rayuwarsu a sansanonin duk da cewa gwamnatin
tarayya na kokari. Yace akwai bukatar a kara
tallafawa 'yan gudun hijiran da suka samu kansu
cikin wannan mawuyacin hali sakamakon rikicin
Boko Haram da ya rabasu da garuruwansu.
Farfasa Al'Amin yace ya fahimci cewa akwai
matsaloli wurin kwana da ruwan sha da kuma
wurin zagayawa. Yace ana karancin wadannan
abubuwa saboda haka ya kwana cikin daya domin
shi ma ya fuskanci abun da 'yan gudun hijiran ke
fuskanta kullum.
Yace rayuwarsu ba za'a ce komi ba saidai a yi
addu'a Allah ya gaggauta lokacin da zasu koma
garuruwansu saboda duk da taimakon da
hukumar bada agajin gaggawa take yi da wasu
hukumomi har da na kasashen waje amma akwai
matsaloli da dama. A rumfar da ya kwana shi
kadai ne amma cikin irinta kusan mutane goma
ne ciki wato kowane mutum yana kwana a takure
ne domin wurin da yake dashi bai fi kafa biyu ba.
Farfasa yace ya kwana a sansanin amma ya kasa
anfani da mazagayarsu saboda halin da take ciki.
Wurin da ake dafa masu abinci bashi da tsafta ko
kadan.
Saboda zafi yace bai iya barci ba dalili ke nan da
ya zagaya da dare inda ya ga wasu suna kwana
kan karfen gado babu katifa. Wasu ma gadajen na
waje ne dare da rana ko kuma an yi ruwa nan
suke kwana.
Akan irin tallafin da yakamata gwamnati ta bayar
tunda ya kwana a wurin, Farfasa Al' Amin yace
'yan gudun hijiran suna ran shugaban kasa to
amma sai an kammala fatattakar 'yan ta'adan a
kawar da abun da ya korosu kana a mayardasu
garuruwansu.
To saidai Farfasa Al'Amin yace hukumarsa ta fito
da wani sabon tsari na soma gina gidaje masu
saukin kudi da kuma ginasu cikin dan karamin
lokaci. Za'a iya kammala ginin gida mai dakuna
uku ko hudu cikin kwana biyar kacal. Wannan
wata fasaha ce daga kasar China wadda yanzu
suna koyawa mutane.