Gwamnatin kasar Rasha ta nuna rashin amincewa da rahoton da aka tattara game da jirgin saman Malesiya da aka harbo a Yukren.
Rasha ta ce, rahoton ya karkata ga bangare daya ne kawai, kuma akwai bukatar a dora alhakin harbo jirgin kan gwamnatin Yukren.
Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Rasha ta ce, rahoton na cike da kurakurai.
Hukumar tsaron jiragen sama ta kasar Holan ta bayyana cewa,an harbo jirgin na Malesiyane a gabashin Yukren da makami mai linzami na kasar Rasha.
A shekarar da ta gabata ne aka harbo jirgin Malesiya dauke da mutane 295 a kan iyakar Rasha da Yukren.