Har yanzu Michel Platini yana son ya maye gurbin Sepp
Blatter a matsayin shugaban Fifa duk da dakatar da shi
da aka yi daga aiki a hukumar.
Kwamitin Da'a na hukumar Fifa ne ya dakatar da
shugaban Fifa Sepp Blatter da sakatare janar Jerome
Valke da kuma Platini daga shiga harkokin Fifa tsawon
kwanaki 90.
An dakatar da Platini ne saboda wani rahoto da Fifa ta
gudanar kan karbar kudi fam miliyan 1.35 daga wajen
Blatter a 2011.
Shugaban hukumar kwallon kafar Turai ya sanar da wata
jarida Le Monde cewa bai aikata ba dai-dai ba, kuma har
yanzu yana son yin takarar kujerar shugabancin Fifa da
za a yi zabe a watan Fabrairu.
Platini ya ce abin kunya ne da ake zarginsa da laifi dai-dai
da wanda ake zargin sauran jami'an Fifa kan cin hanci da
rashawa.
Ya kuma ce lauyoyinsa na bin bahasin batun sau da kafa,
za kuma su shigar da kara ga kotun daukaka kara ta
wasanni ta duniya da zarar lokacin yin hakan ya yi.
Title :
Platini na takaicin dakatar da shi daga Fifa
Description : Har yanzu Michel Platini yana son ya maye gurbin Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa duk da dakatar da shi da aka yi daga aiki a hukumar...
Rating :
5