Daya daga cikin makarantun Almajirai wadanda gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ta gina a Katsina, Jihar Katsina. An maida su wajen kiwon shanu da aka kwato daga hannun Barayin shanu.
Makarantar wadda ke kusa da Barikin Soja ta Katsina dake kan hanyar zuwa Jibiya an gina ta ne domin ta zama muhalli ga Almajirai da Malaman su domin su koyi ilimin addini dana zamani kuma a hana yawan bara, roko da kuma tallace tallace.
Idan za’a iya tunawa Majalisar Dinkin Duniya ta fidda wani rahoto wanda ke nuna cewa akwai sama da yara Miliyan 11 da basu zuwa makaratna a Najeriya wanda kusa kashi 70 daga Arewa ne, jihohin Katsina, Kano da Kaduna.
Satar Dabbobi babbar matsala ce musamman a Yankin Yammacin Katsina wajen karamar hukumar Batsari. Rahoto ya nuna cewa sama da shanu 10,000 aka sace tun daga farkon wannan shekarar.
Wasu wadanda aka sace ma dabbobin sun zo sun nuna shaida an basu abun su. Wadansu su kuma na nan na jiran masu su. Wajen dai yan sandan Najeriya ke gadin shi.
Ga hotunan daga can a kasa: