Shugaban Amirka Barack Obama ya nemi afuwar kungiyar likitocin komai da ruwanka sakamakon kashe fararen hula 22 da sojin Amirka suka yi a wani hari ta sama da suka kai a Afganistan.
Shugaban kungiyar Dr. Joanne Liu ya ce, shugaba Obama ya kra su ta waya tare da neman afuwarsu bisa afkuwar lamarin wanda ya janyo mutuwar liktocin kungiyar da ma marasa lafiya.
Ya ce, daga baya, Obama ya kira shugaban kasar Afganistan Ashraf Gani inda ya mika ta'aziyyarsa gare shi.
An kashe likitoci da ma'atan kungiyarsu da marasa lafiya bisa kuskure a yayin wani hari ta sama da sojin Amirka suka kai a jihar Kunduz da 'yan kungiyar Taliban suka kwace.