Wanda yake mataki na daya a jerin wadanda suka fi iya
kwallon tennis a duniya Novak Djokovic ya lashe gasar
China Open.
Djokovic ya lashe gasar ne, bayan da ya doke Rafael
Nadal da ci 6-2 da kuma 6-2 a fafatawar da suka yi a
China.
Wannan kuma shi ne karo na shida da Nadal ya buga
wasan karshe a gasar kwallon tennis daban-daban da ya
yi a shekarar 2015.
A karawar mata da aka buga wasan karshe a gasar,
Garbine Muguruza ce ta dauki kofin bayan da ta doke
Timea Bacsinszky.
Title :
Novak Djokovic ya lashe gasar China Open
Description : Wanda yake mataki na daya a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya Novak Djokovic ya lashe gasar China Open. Djokovic ya lashe...
Rating :
5