Malik bn Dinaar (rah) - yana daga cikin manyan magabata na kwarai wadanda suka shahara sosai wajen Gudun duniya da tsantseni da kuma tsayawa wajen bautar Allah ba dare ba rana.
Watarana cikin dare yana sallah sai wani barawo ('Dan fashi) ya haura ta katangar gidan domin yin sata. ya zagaya duk cikin gidan bai samu komai ba. Sai yaga Maigidan yana sallah. (Wato Malik din kenan).
Nan da nan sai Malik bn Dinaar ya idar da sallar sannan ya juya wajen 'Dan Fashin yayi masa sallama sannan yace masa:
"Ya kai 'Dan uwana!! Allah shi gafarta maka. ka shigo min gida ba tare da izini ba, Ka zagaya amma baka samu abinda zaka dauka ba. Ni kuwa ba zan kyaleka ba, Har sai ka aikata mun wata fa'idah".
Ya tashi ya kawo masa ruwa acikin Kwarya, sannan yace : "Tashi kayi alwala kayi sallah raka'a biyu. Na tabbata zaka samu alkhairin da yafi dukiyar da zaka sata".
Sai Barawon yace "To madalla". ya tashi yayi alwala ya sallaci raka'a biyu, yayi sallama. Sannan yace "Ya Maliku, shin kana ganin babu damuwa agareka, In Qara wasu Raka'o'in guda biyu?"
Sai Malik yacr masa "Ci gaba da sallah gwargwadon yadda Allah ya baka ikon yi". 'Barawon nan bai gushe yana ta sallah ba, har sai da asubah tayi. Sai Malik yace masa "Tashi ka tafi, Allah ya shiryaka".
Sai barawon ya sake neman alfarma yace masa "YA SHUGABANA Idan ba zaka damu ba, zan so kayi min izini yau in zauna wajenka. Domin na riga na dauki niyyar yin azumi ne".
Sai Malik yace masa "Na yarda ka zauna anan gwargwadon yadda Allah ya baka iko". Don haka 'Dan fashin nan ya zauna tsawon wasu kwanaki masu yawa. Yana ta yun azuminsa da Qiyamullaili.
Ranar da zai tafi sai yace masa "Ya Malik, nifa na riga nayi niyyar tuba daga dukkan abinda na aikata". Sai yace masa "Ai wannan ahannun Allah yake". Nan dai barawo ya tuba, Kuma Allah ya kyautata tubansa.
Rannan sai suka hadu da wani Kasurgumin 'Dan Fashi wanda suke yin satar tare dashi. Sai yace masa "Ya kai abokina! (kwana biyu bani ganinka) Ai nayi zaton ka Tsinci wata Taskar Arziki ne".
Sai shi kuma yace "A'A na tsinci Malik bn Dinaar ne. Naje domin inyi masa sata, sai shi kuma ya sache ni. Domin yanzu haka ni na riga na tuba zuwa ga Allah, Kuma zan Lazimci Kofar Allah din. Zanyi ta kwankwasa masa har sai ya bude min. Har sai na samu irin abinda Masoyan Allah suke samu".
*************************
DAGA ZAUREN FIQHU
Allahu Akbar!!! Wadannan sune bayin Allah na kwarai wadanda kullum burinsu shine su kama hannun mutane su sada-su da Allah.
Basu kore ma Allah bayinsa, kuma basu Qin bayin Allah saboda Zunubinsu ko Son zuciya.
Wallahi ba zamu samu yardar Allah ba har sai mun so junanmu, Mun hada kanmu. Mu dena Kyama da zagin junanmu. Ba kai keda Hisabi ba, ballantana kace su wane duk 'Yan wuta ne.
Jama'a muji tsoron Allah mu kyautata mu'amalarmu da sauran Musulmai, Shiryayyunsu da masu laifin. Da wadanda muka samu sabanin fahimta dasu akan wani reshe na addini.
Yin haka zai sanya Musulunci ya samu kwarjini da bunkasa aduniya.
Wannan nasihar tazo ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (5)
v