Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasan Najeriya ya bayyana cewa Najeriya zata yi nasarar murkushe yan Boko Haram kamar yadda ta murkushe yan a waren Biafra.
Yakin Biafara ya auku me a 1967 – 1970 a lokacin da wasu jihohi daga Kudu maso Gaba da kuma maso Kudu suka so su balle daga Najeriya domin su kafa kasar su “Biafra”.
Jaridar Daily Trust Ta ruwaito cewa tsohon shugaban Kasa ya bayyana Haka be a lokacin da ya gabatar da masa a sha’anin Tsaro a shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gafara shugaban Kasa domin su sanar da Najeriya yadda kasar su Columbia ke yakar Yan ta’addan Ta na FARC.
Obasanjo ya bayyana cewa ba sai an kashe duka yan Boko Haram ba sannan za ace anyi nasara a kansu. Da zarar sojojin Najeriya suka samu nasara akan su to naci nasara, cewar Obasanjo. Yace:
“Kamar yadda yan Columbia suka ce, ba sai an kashe duka yan Boko Haram ba sannan aka samu nasara. Da zarar sojoji suka samu Babban nasara Akan su shike nan. Sauran aiyuka irin su taimakon tattalin arziki, basu ilimi da sauran su zasu biyo baya.”
Kuma ya bayyana cewa wa’adin watanni 3 da shugaban kada ya bawa sojoji zaya taimaka kwarai wajen cin nasara akan su.