Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta ce ta kamala jigilar
alhazan kasar zuwa gida , kwana hudu kafin wa'adin da
aka debar mata ya zo karshe kuma kwanaki 7kafin a rufe
filin saukar jiragen sama na sarki Abdulaziz da ke jedda.
A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Abdullahi
Mukthar ya aikewa BBC ta ce wannan shi ne jigila mafi
sauri a yan shekaru baya bayanan.
A baya Najeriya ta rika fuskantar matsala wajen jigilar
alhazai zuwa kasa mai sarki ko dawo da su gida.
Sai dai 'yan Najeriya da dama suka rasa rayukansa a aikin
hajjin ba ya yinda wasu suka ji raunuka a turmitsitsin da
ya faru a ranar arafa da kuma fadowar kugiya mai daukar
kaya mai nauyi.