Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce bayan an kwashe wadanda hare-haren Nyanya da Kuje suka shafa zuwa asibiti, an tabbatar da mutane 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da 41 suka jikkata.
Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar Abuja, Ishaya Chonoko, ya yi karin bayani da cewa a Nyanya, mutane uku ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata; a Kuje kuma mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da 21 ke samun kulawa a asibitoci.
Mista Chonoko ya kuma ce Darakta Janar na hukumar Muhammad Sani Sidi ne ya jagoranci kwashe mutanen da abin ya shafa. Tuni dai gwamnati ta ce ta dauki nauyin biyan kudin asibitin.
Ita kuwa hedkwatar rundunar 'yan sanda ta Najeriyar cewa ta yi binciken farko da ta gudanar ya nuna cewa 'yan kunar-bakin-wake biyu ne, mace da namiji, suka kai hare-haren.
Rundunar 'yan sandan, a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai magana da yawunta, ACP Olabisi Kolawole, ta ce tuni Sufeto Janar na 'yan sanda Solomon Arase ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen yankin na Babban Birnin Tarayya, FCT.
A daren jiya ne dai aka kai hare-haren da misalin karfe goma a wata tashar mota da ke Nyanya, da kusa da wani ofishin 'yan sanda a Kuje, da kuma wata kasuwa a garin na Kuje.
Title :
Mutum 18 ne suka mutu a hare-haren Abuja
Description : Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce bayan an kwashe wadanda hare-haren Nyanya da Kuje suka shafa zuwa asibiti, an tabba...
Rating :
5