Shugaban Amurka, Barrack Obama ya ce dole ne 'yan
kasar su hada kansu domin dakile yawan harbe-harben
da ake samu a Amurkar.
Yana magana ne bayan ganawa da iyalan mutanen da
aka harbe har lahira a wata kwaleji jihar Oregon a makon
da ya gabata a inda wani dalibi ya harbe mutane tara
kafin kuma daga bisani ya harbe kansa.
Sai dai kuma kafin tattaunawar, masu rajin kare hakkin
amfani da bindiga sun yi wata zanga-zangar limana a filin
jirgin saman na Oregon suna masu daga rubuce rubece
dake cewa 'ba ma maraba da Obama'.
Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wasu karin
jerin harbe-harben da aka yi a jami'o'i da ke jihohin
Arizona da Texas na Amurkar ranar Juma'a.
Title :
'Harbin mutane ya zama ruwan dare a Amurka'
Description : Shugaban Amurka, Barrack Obama ya ce dole ne 'yan kasar su hada kansu domin dakile yawan harbe-harben da ake samu a Amurkar. Yana mag...
Rating :
5