Shugaban Kastam, Kanar Hameed Ali Mai murabus ne ya bayyana haka, inda yace duk wanda akayi ma karin girma ta haramtacciyar hanya, za’a rage mashi mukami.
A cewar Jaridar Vanguard, shugaban ya bayyana cewa za’ayi gyaran cikin gida wanda zaya iya sanya dubunnai su rasa aikin su.
Kanar Hammed Ali Mai murabus ya bayyana haka ne a makarantar kastam dake a Ikeja, birnin jihar Legas inda yace: “A koyaushe idan muna tattaunawa da jami’ai na ina gaya masu cewa na lura akwai matsaloli da yawa a hukumar.
“Zamu nada kwamiti wanda zaya duba haka. Idan anyi ma mutum karin girma kamar yadda ya kamata, to shike nan. Idan kuma saboda Ubangida ne to zamu soke shi.”
Inda yake magana akan alfarmar da ake ba masu shigo da kaya, shugaban kastam din sai yace ” alfarmar nan tafi karfin mu, mun gode Allah shugaban kasan nan ya hana ta. Yace: “Alfarma kawai sai dai ga Jakada kamar yadda doka ta shinfida, Ko kuma daga majalisar dinkin duniya.”
Title :
Mutane Da Yawa Zasu Rasa Aikin Su A Hukumаr Kastam
Description : Shugaban Kastam, Kanar Hameed Ali Mai murabus ne ya bayyana haka, inda yace duk wanda akayi ma karin girma ta haramtacciyar hanya, za’a rage...
Rating :
5