Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce
mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da
aka kai a sansanin 'yan gudun hijra da ke Yola a jihar
Adamawa.
Lamarin ya auku ne sansanin 'yan gudun hijira da ke
Malkohi a cikin Yola.
Babban jami'in watsa labarai na hukumar, Sani Datti, ya
ce mutane 20 kuma sun jikkata.
A cewar sa, an bai wa bakwai daga cikin wadanda suka
jikkata magunguna, kana aka sallame su; yayin da
mutane 13 -- cikin su har da jami'an hukumar guda hudu
-- ke ci gaba da samun kulawa a asibitin Tarayya da ke
Yola.
Daruruwan mutane ne ke zaune a sansanonin kula da
'yan gudun hijirar sakamakon aika-aikar da 'yan Boko
Haram suka yi.
A baya dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a
garin na Yola.
Title :
Mutane bakwai sun rasu a sansanin 'yan gudun hijira
Description : Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijr...
Rating :
5