Hukumomi a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin
Najeriya sun ce mutane 30 ne suka mutu a harin bam din
da aka kai a birnin Yola.
Kakakin gwamnatin jihar, Ahmed Sajo, ya shaida wa BBC
cewa mutane 96 ne suka samu raunuka.
Ganau sun ce an tayar da bam din ne a Masallacin
Jambutu da ke Jimeta a daidai lokacin da ake tayar da
Sallar Juma'a.
Sajo ya ce 'yan kunar bakin wake ne suka tashi bama-
baman bayan an tayar da Sallah.
Title :
Mutane 30 sun mutu a harin Yola
Description : Hukumomi a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane 30 ne suka mutu a harin bam din da aka kai a birnin Yola. Kakak...
Rating :
5