Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu sannan wasu da ba a san yawansu ba sun jikkata sakamakon hare-haren kunar-bakin-wake guda biyu, a wani Masallaci da ke unguwar Mola, a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da yammacin ranar Alhamis.
Shugaban hukumar ta NEMA mai kula da shiyyar arewa maso gabshin Najeriya, Muhammad Kanar ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a kai ga tantance yawan mutanen da suka samu raunuka ba sakamakon harin.
Sai dai kuma ya ce akwai mutane guda bakwai wadanda suka samu raunuka masu tsananin gaske.
Wani kuma wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru ya shaida wa BBC cewa wasu mutane guda biyu suka zo masallacin bayan an tayar da sallar Magriba a inda na farko ya tayar da bam a cikin masallacin.
Shi kuma na biyun wanda yake wajen masallacin ya tayar da bam din da ke jikinsa a lokacin da mutanen da ke waje suka yi kokarin kai wa na cikin masallacin dauki.
Ko a daren ranar Talata ma 'yan kunar bakin wake sun tayar da bama-bamai a unguwar Ajilari inda mutane bakwai ne suka mutu sannan mutane 11 suka jikkata.
Mutane kusan 150 aka kashe ko kuma aka jikkata a fashewar wasu abubuwa irin wannan a Maiduguri, makonni hudu da suka gabata.
Wannan harin ya zo ne a lokacin da rundunar sojin Najeriya ke ikirarin samun nasara a kan kungiyar Boko Haram.
bbchausa