Louis van Gaal ya ce da zarar Manchester United ta doke
Manchester City a gasar Premier da za su yi a ranar
Lahadi, suna daga cikin wadanda za su iya lashe kofin
bana.
United din ta doke Everton da ci 3-0 a Goodison Park a
ranar Asabar, yayin da Manchester City ta lallasa
Bournemuth da ci 5-1 a Ettihad.
Morgan Schneiderlin da Ander Herrera da kuma Wayne
Rooney ne suka ci wa United kwallaye ukun a karawar.
Van Gaal ya ce harin da suke yi shi ne su zama zakaru,
kuma abu ne mai mahimmaci da suke son cimma.
Ya kuma kara da cewar ya ji dadi da yadda 'yan wasa
suka murza leda da kwazon da suka yi, yana mai alfahari
da su.
Kocin ya kuma kara da cewar ya kamata su dora a kan
kokarin da suke yi, "Kuma da zazar mun doke City a
wasan gaba, zan gamsu da cewar za mu iya lashe kofin
Premier bana", in ji shi
Title :
'Za mu dauki Premier idan muka doke Man City'
Description : Louis van Gaal ya ce da zarar Manchester United ta doke Manchester City a gasar Premier da za su yi a ranar Lahadi, suna daga cikin wadand...
Rating :
5