Miyetti Allah kungiyar Fulani ta kasa ta mayarwa
Yarbawa martani akan wa'adin makwanni biyu da
suka ba Fulani da su kwashe nasu- i- nasu su koma
inda suka fito.
Yarbawan sun baiwa Fulani
wa'adin ne sakamakon zargin cewa su Fulani ne
suka yi garkuwa da tsohon sakataren gwamnantin
tarayyar Najeriya Chief Olu Falae.
Alhaji Muhammad Kirwa Ardon Zuru shugaban
kungiyar Fulani ta Najeriya wato Miyetti Allah
yace babban martanin da suke son su maida suna
son Yarbawa su sani Olu Falae ba shugaban
Yarbawa ba ne kawai. Ya taba zama sakataren
gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ya mulki
kowace kabila a Najeriya.
Batun koro wani daga kudu zuwa arewa ba zai
haifar wa kasar da mai ido ba, inji Alhaji Kirwa.
Yace yanzu tunanen Najeriya shi ne dinke barakar
da ta taso a wasu wurare saboda a samu zaman
lafiya.
Gwamnatin yanzu kokari ta keyi ta samar ma
kasar zaman lafiya.
Dattijon Fulani Muhammad Dodo Oroji ya kira
majalisar kasa ta yi wani abu. Yace abun da a keyi
a Najeriya abun takaici ne. Yace duk dan Najeriya
na iya zama inda ya ga dama. Ya kira masu ikon
kasar su hukunta duk wani wanda zai yi irin
kalamun da Yarbawa suka yi.
Kwararre a harkokin tsaro Birgediya Sale Bala
mai ritaya yace akwai mafita. Yace Najeriya ta
zama kasarmu gaba daya. Ya kamata a manta da
batun kabilanci ko bangaranci ko addini. Kowa na
iya zama inda ya ga dama amma dole ne ya
mutunta al'ada da akidar mutanen da ya je ya
zauna cikinsu. Yace saboda haka a dinga yin
furucin da zai hada kawunan 'yan kasar. Yarbawa
da 'yan arewa sun dade suna tare kuma babu
wanda ya fi Yarbawa jin dadin saniya. Inji Sale
Bala abu ne da ya faru amma ba'a yi zurfin
tunane a kansa ba.
Matakin da majalisar waikai ta dauka jiya tamkar
mayarda martani ga takaddamar dake tsakanin
Yarbawa da Fulani a kudancin kasar ne. Majalisar
ta umurci gwamnatin tarayya ta yiwa Fulani
makiyaya burtuloli domin magance yawan
rigingimu tsakanin makiyaya da manoma da
yanzu ya mamaye jihohin arewa kuma yana
neman ya kai kuduancin kasar