Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana sunayen
da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ma ta
don tantancewa.
Yau ne Shugaban Majalisar
Dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya
karanta sunayen Ministocin da Shugaba
Muhammadu Buhari ya mika ma Majalisar don
tantancewa. Wakiliyarmu a Abuja Madina Dauda
ta ruwaito Shugaban Majalisar Dattawan na cewa
karanta sunayen Ministocin, wadanda su ka hada
da: Abubakar Malami, daga jahar Kebbi; da Janar
Abdurrahman Bello Danbazau daga jahar Kano;
da Aisha Jummai Alhassan, daga jahar Taraba; da
Alhaji Laye Muhammed; da Babatunde Raji
Fashola daga jahar Lagos; da Barrister Adebayo
Shittu; da Barrister Solomon Dalong, daga jahar
Filato.
Sauran mutanen da aka gabatar da sunayensu don
tantancewar sun hada da Sanata Chris Ngige daga
jahar Anambra; da Rotimi Amaechi, jahar Rivers;
da Chief Audu Innocent Ogbeh, daga jahar Kogi;
da Mrs Amina Ibrahim; da Dr. Osage ENARE da Dr
Emanuel Ebe Kachukwu da Dr Kayode Fayemi ,
jahar Ekoiti; da Injiniya Suleiman Adamu da Mrs
Kemi Adiosun; da Dr. Ogbunaya Onu, jahar Abia;
da Ahmed Isa Ibeto, daga jahar Nasarawa; da
Ibrahim Usman Jibrin da Sanata Hadi Sirika, daga
jahar Katsina; da Sanata Udoma Udo Udoma, daga
jahar Akwa-Ibom.
Tuni dai aka fara cece-kuce kan sunayen. Wani
Sanata dan jam’iyyar PDP y ace da sun yi
tsammanin za a gabatar da sunayen wasu sabbin
mutane ne, to amma sai gashi mutanen da su ka
sani ne. Hasalima, in ji shi, wasunsu sun yi aiki
tare. Y ace duk da haka za su gayyaci hukumomin
ICPC da EFCC su binciki kowannensu.
Shi kuwa wani dan jam’iyyar APC Sanata
Mohammed Shaba Lafiagi y ace za a bi tsarin da
aka saba bi ne wajen tantancewar.
Madina ta ce ranar Talata mai zuwa 13 ga wata ne
za a yi tantancewar.
Title :
Ministoci: Shugaban Majalisar
Dattawan Najeriya Ya Karanta
Sunayen Da Za A Tantance
Description : Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana sunayen da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ma ta don tantancewa. Yau ne Shugaban Majalisar Da...
Rating :
5