An danganta dawowar matsalar mai a sassan
Najeriya da wasu matakan da aka dauka da kuma
rashin bayar da hadin kai daga ainihin inda ake
sayo man.
Matsalar karancin man
fetur ta soma dawowa wasu sassan arewacin
Najeriya, inda ake ganin dogayen layuka a
wuraren da ake da dan man. Wakilnmu a Minna
Mustapah Nasiru Batsari y ace tun a farkon makon
jiya aka wayi gari babu man a galibin tasoshin
man da ke arewacin Najeriya.
Mustapha y ace a Minna, babban birnin jahar ta
Naija babu karancin man, to amma akwai
matsalar a wasu sassan jahar. Wani mai suna
Umar Adam Faruk daga Kwantagora ya shaida ma
Mustapha ta waya cewa akasarin gidajen mai sun
rufe inbanda Total da NNPC. Shi ma wani mai
suna Alhaji Aliyu Isa daga wani sashin jahar y ace
bas u da man. Don haka Mustapha ya tuntubi
Shugaban kungiyar Dillalan man fetur a Najeriya
Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari, wanda ya
tabbatar rashin man a wasu gidajen man,
al’amarin da ya alakanta da rashin man a
wuraren da ake zuwa dauko – ciki har da Lagos
da wasu depot-depot. Bugu da kari, in ji shi,
kungiyarsu ta umurci mambobinta cewa kar su sai
da mai saboda za su fadi kan farashin da
gwamnati ta umurce su su sayar, wato kan Naira
87, alhalin kuwa, sabanin cewa da gwamnati ta yi
a rika sai da masu man kan Naira 77 da sulai 6;
ana saida masu shi ne akan Naira 82. Wannan, in
ji shi, ya sa ‘yan kasuwa da dama sun ji tsoron
sayo man saboda gudun faduwa.
Title :
Matsalar Karancin Mai Ta Fara
Dawowa
Description : An danganta dawowar matsalar mai a sassan Najeriya da wasu matakan da aka dauka da kuma rashin bayar da hadin kai daga ainihin inda ake s...
Rating :
5