Matasan kungiyoyin Fulani na Miyetti Allah da
Kautal Hore sun hada kai sun kafa wata kungiya
da zata dinga wayar da kawunan Fulani domin
samun cigabansu.
Manufar sabuwar kungiyar ta
Junde Jam Fulani Association of Nigeria itace
hadin kan matasa domin yin tafiya daidai da
zamani da kuma kwato wa Fulani hakinsu.
A cewar shugaban sabuwar kungiyar Abdullahi
Maikano kungiyar zata dukufa wajen hadin kan
matasa ne.Yace babu wani mutum dake da
hankali da zai goyi bayan kisa ko sata. Rashin
shugabanci nagari ya hana a kira matasan a tsayar
da magana daya. Sai an san abun dake faruwa
kafin a ce za'a dauki mataki.
Mataimakin kungiyar Abdulkarim Bayero yace
zasu hada kan matasa domin mika korafinsu ga
gwamnati. Zasu wayar wa matasansu kai ta fannin
ilimi. Dangane da sace sacen shanu da suka
haddasawa Fulani hasarar dukiyoyinsu, yana son
gwamnati ta taimaka ta rage masu hasarar.
Muhammad Lawal Ardo Haruna yace cigaba ne a
samu kungiyoyi da dama. Kungiya daya ba zata
wadatar da bukatun Fulani ba. Yawansu shi ya fi
a'ala.
Tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen
Filato Inusa Jibrin Jagaba ya ba sabuwar kungiyar
shawara. Yace su kasance masu da'a da sanin
yakamata. Su dinga kiran matasa saboda su san
abubuwan dake faruwa.