TAMBAYA TA 1738
********************
AS-SALAMU ALAIKUM, MALAM wani tambaya ce gare ni kamar haka: Wai a hadisi ko tarihin magabata akwai laififukan da macce zatayi wa mijina ta har ta kai ga mijin ta ba zai iya cin abincinta ba? kuma ko yaci ba zai iya ci da farin ciki har ya koshi ba, Da zarar yaci nama tsoka daya ko biyu haka ma abinci in ya samu loma daya ko biyu ba zai iya cigaba da cin abincin ba kuma ko yana jin yinwa ne?
Dalilin da yasa nayi wannan tambayar wani salihin bawan Allah ne ya fada cikin wannan matsalar kuma yaki ya gayawa wani lafufukan da matar tasa take yi masa wani lokaci in aka kawo masa abincin sa da zaran ya bude ya fara ci kadan sai ya rufe in yaga almajiri sai ya bashi abincin wani lokaci sai ya je ya samu bread da minerals yaci.
Sai watarana na tuntubeshi yace min gaskiya ba zai iya gayawa wani laifufukan da matar sa take yimasa ba domin duk wanda yaji laifufukan ta toh ba zai kalleta da mutunci ba, yace domin akwai watarana ya dauketa suka je can gidan iyayen ta ya sarnarwa iyayen ta abinda ke faruwa tsakaninsa da matarsa, iyayenta sukaiyi mata fada da magaggannu makamantan tsinuwa yace don hakane ma baya so ya gaya ma wani laifufukan ta, amma shima maigidan yace yana hakuri da ita ne albarkaci 'ya'yan ta domin sunada yara biyu. Toh yace albarkaci wadannan yaran ne yake hakuri da ita, toh wai yaya irin wannan zamantakewar take a musulunce ?? Kuma malam irin wannan hakurin tana da lada??? Daga wani almajiri, Allah ya bada ikon amsa!.
AMSA
*******
Wa alaikumus Salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Lallai duk yadda akayi, wannan matar tasa ta chutar dashi ne sosai. Kuma abin yana da girma sosai tunda kaga shi da kansa ya kasa gaya maka. Don haka kar ka matsa masa cewa sai ya gaya maka. Kai dai kaci gaba da bashi hakuri.
Addininmu na Musulunci ya bama Miji damar daukar matakan ladabtarwa akan matarsa idan ta zama marar biyayya gareshi. Allah yana cewa:
"WADANNAN (MATAYEN) DA KUKE TSORON BIJIREWARSU, TO KUYI MUSU WA'AZI, KUMA KU KAURACE MUSU AWAJEN KWANCIYA, KUMA KU BUGESU".
Al Imam Ibnu Katheer yace: "Duk lokacin da Miji yaga alamomin bijirewa daga bangaren matarsa, To ya wa'azantar da ita, ya tsoratar da ita Uqubar da zata risketa cikin sa'bon Allah. Domin kuwa Allah ya riga ya wajabta mata Hakkin Mijinta akanta tare da biyayyarsa. Kuma ya haramta mata sa'ba masa. Saboda falala da fifikon da shi Mijin nata yake dashi akanta.
Domin Manzon Allah (saww) yace: "DA ACHE ZAN UMURCI WANI YAYI SUJJADAH GA WANI, WALLAHI DA NA UMURCI MACE TAYI MA MIJINTA SUJJADAH SABODA GIRMAN HAKKINSA AKANTA".
Idan kuma laifin da take yi masa ta bangaren hanashi saduwa ne, to ya isar mata da Qaulin Manzon Allah (saww) wands yake cewa:
"IDAN NAMIJI YA KIRA MATARSA ZUWA GA SHIMFIDARSA, AMMA TAQI YARJE MASA, TO MALA'IKU ZASU RIKA TSINE MATA HAR GARI YA WAYE".
(Bukhary hadisi na 5,194. Muslim hadisi na 1,436).
Idan kuma cin amanarsa take yi, tana cin amanarsa acikin dukiyarsa, ko kuma akan kanta, Wato tana yi masa sata, ko kuma tana kula wasu Mazajen banza, To hakika ta shiga layin matayen da ba zasu samu albarkar rayuwa ba. Kuma sha azaba mafi radadi awutar jahannama sai dai idan ta tuba.
Idan duk bata ji wannan wa'azin ba, To daga nan sai ya Qaurace mata ya dena kwanciyar aure da ita. Ya dena yi mata magana sai kadan kadan. Kamar yadda Aliyu bn Abi Tal'ha ya ruwaito daga Abdullahi Bn Abbas (ra).
Idan kuma duk wannan bai isheta ba,To Allah ya bashi damar ya daketa. Amma irin dukan nan wanda ba zai kumbura mata jiki ba, Kuma kar ya karya mata Qashi ko targade.
Hakika tun azamanin Manzon Allah (saww) da lokacin Sahabbai da tabi'ai ana samun rikici tsakanin ma'aurata. Shi yasa ma Allah ya saukar da wadannan ayoyin na cikin Suratun Nisa'i (34-35).
Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.