Masarautar Suleja ta nisanta kanta daga shiga duk
wasu alamura na siyasa a jihar Neja ko a tarayya.
Masarautar dake cikin jihar
Neja ta kuma isanta kanta daga duk wata
jam'iyyar siysa. Ta rungumi "'yan babu
ruwanmu".
A wani taron manema labarai masarautar ta ce
hankalinta ya tashin akan wasu kalamun batanci
ga masarautar da wani dan siyasa ya rika bazawa.
Tace lamarin baraza ne ga zaman lafiyar yankin.
Alhaji Yusuf Baba Dan Galadiman masarautar
wanda kuma shi ne hakimin Kabula shi ya yi
magana a madadin sarkin Suleja Malam
Muhammad Lawal Ibrahim. Yace ita masarauta
uwa ce ga kowa. Yace duk wata jam'iyya da
gwamnati ta san da ita ashirye suke su karbeta
domin a samu cigaban gari.. Ya kira jama'a da su
bi jam'iyyar da suke so ba tare da wani
tsangwama ba.
Musabbabin wannan kashedin shi ne kalamun
batanci da wani dan siyasa ya keyi sanoda wai ya
nemi wata sarauta a masarautar. Mutumin ya
kuma zargi sarkin Suleja Mohammad Awal
Ibrahim da yin magana da wasu manyan jihar.