Dan kwallon Manchester United Anthony Martial, ya
lashe kyautar gwarzon dan kwallon gasar Premier na
watan Satumba.
Dan wasan mai shekaru 19, ya zura kwallaye uku cikin
wasanni hudu a watan da ya wuce.
Martial shi ne dan wasa mafi tsada mai kankantar
shekaru a duniya, inda aka siyo shi daga Monaco a kan
fan miliyan 36.
Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino shi ne ya lashe
kyautar a bangaren masu horadda 'yan kwallo.
Cikin nasararsa hadda wasan da suka doke Man City da
ci hudu da daya a White Hart Lane.
Title :
Martial ya lashe kyautar watan Satumba
Description : Dan kwallon Manchester United Anthony Martial, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon gasar Premier na watan Satumba. Dan wasan mai shekaru...
Rating :
5