Yau da wasu ‘yan makwanni da suka gabata, garin Maiduguri ya zama wani dandali na kai hare haren kunar bakin waken kungiyar Boko Haram, da yayi sanadiyar hasarar rayukan fararen hula da dama.
Wannan dai na faruwa ne, a dai dai lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ke sake jaddada aniyarsa ta ganin nan da karshen wannan shekara ta 2015 dakarun Sojan kasar su kawo karshen tashe tashen hankullan da mayakan na Boko Haram ke haddasawa a kasar
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sama da mutane 34 nesuka rasa rayukansu, a cikin wani jerin hare-haren kunar bakin wake, da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai a birnin na Maiduguri, babban birnin jihar Borno, dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya
Title :
Maiduguri ya zama dandalin hare haren kunar bakin waken mayakan Boko Haram
Description : Yau da wasu ‘yan makwanni da suka gabata, garin Maiduguri ya zama wani dandali na kai hare haren kunar bakin waken kungiyar Boko Haram, da y...
Rating :
5