Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu mata 'yan
harin kurnar bakin-wake su hudu da ake zargin 'yan
kungiyar Boko Haram ne sun tayar da bam da ke jikinsu
daya bayan daya a unguwar Sajeri da ke birnin Maiduguri
a ranar Alhamis.
Wata sanarwar da kakakin rundunar, Kanal Sani
Kukasheka Usman ya aikewa BBC ta ce uku daga cikin
'yan ta'addan sun tayar da bam dinsu ne a unguwa daya,
yayin da ta hudu ta tayar da nata a gaban wani masallaci.
Kanal Usman ya ce ya zuwa yanzu mutane akalla 14 ne
suka rasa rayukansu -- ciki har da 'yan kurnar-bakin-
waken yayin da mutane 39 suka jikkata.
Ya yi kira ga mutane -- musamman wadanda ke zama a
wuraren da lamarin ya faru --da su kwantar da hankalinsu
kuma su ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke wakana
a kewayensu, yana mai cewa soji suna yin duk abin da
kamata domin tabbatar musu da tsaro.
Sanarwar ta ce abu ne mai muhimanci a tabbatawar wa
al'ummar yankin da cewa duk da kokarin da mayakan
kungiyar Boko Haram suke yi wajen mayar da hannu
agogo baya a ci gaban da ake samu wajen dawo da
zaman lafiya da kuma tsaro a cikin kasar, ba za su yi
nasara ba.
Title :
'Yan kunar-bakin-wake sun kashe mutane 14 a
Maiduguri
Description : Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu mata 'yan harin kurnar bakin-wake su hudu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun...
Rating :
5