Majalisar dokokin Nigeria ta gindaya sharuɗɗan da za ta
bi wajen tantance mutanen da Shugaba Muhammadu
Buhari ya aika domin nada su a matsayin ministoci.
Daya daga cikin sharuɗɗan shi ne cewar duk wanda za a
tantance sai ya nuna takardar bayanin dukiyar da ya
mallaka.
Mai magana da yawun majalisar dattijan, Sanata Dino
Melaye wanda ya bayyana haka ga manema labarai a
Abuja, ya kara da cewar dole ne sai sanatoci biyu daga
jihar mutum na asali sun amince da shi, kafin majalisar
ta amince a nada mutum a matsayin minista.
A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba ne, majalisar ta ce za
ta soma tantance mutanen.
A makon da ya wuce ne shugaba Muhammadu Buhari ya
aike wa majalisar dattijai sunayen mutane 21 domin a
tantance su kafin, ya nada su a matsayin ministoci.
Title :
Kun san sharuɗɗan tantance ministocin Nigeria ?
Description : Majalisar dokokin Nigeria ta gindaya sharuɗɗan da za ta bi wajen tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika domin nada su a mats...
Rating :
5