Ana ci gaba da samun korafe-korafe a kan wasu daga
cikin sunayen da shugaba Muhammadu Buhari ya
gabatar wa majalisar dattawa domin nada su a matsayin
ministoci.
Na baya-bayan nan shi ne korafin da jam'iyyar APC
reshen jihar Sokoto ta gabatar idan take adawa da bai wa
Hajiya Aisha Abubakar mukamin minista daga jihar.
A cikin wata takardar koke da jam'iyyar ta rubuta wa
shugaban kasar bayan wani taron da gwamnan jihar
Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, reshen jam'iyyar ya
ce Hajiya Aishatu Abubakar ba ta da katin zama mamba
ta kowace jam'iyya, abin da ya sabawa sashe na 62 sakin
layin na biyu na kundin tsarin mulkin kasar.
Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin wasu masu
goyon bayan ta ke ci gaba da zanga-zangar lumana da
kuma taruka da 'yan jarida domin nuna rashin
amincewarsu ga nema sauya sunanta.
'Shiyyoyin Siyasa'
Can kuma a jihar Yobe, wasu kungiyoyi sun gabatar da
korafi a kan mika sunan Hajiya Khadija Bukar Abba
Ibrahim a matsayin minista inda suka ce hakan ya
sabawa tsarin rarraba mukamai a tsakanin shiyyoyin
siyasar jihar.
A cewar su, da Hajiya Khadija da kuma gwamnan jihar,
Ibrahim Gaidam duk 'yan shiyyar siyasa ta Yobe ta gabas
ne, kuma mijinta, watau Sanata Bukar Abba Ibrahim shi
ne sanata da ke wakiltar shiyyar.
Dama dai ana gabatar da korafe-korafe a kan mika sunan
tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma
mutumin da aka gabatar da sunansa daga jihar Oyo,
watau Barrister Adebayo Shittu.
A ranar Talata ne ake sa ran majalisar za ta koma zaman
ci gaba da tantance mutanen da shugaba Buhari ke son
nada wa a matsayin ministoci.
A ranar Alhamis da ta wuce ne, majalisar dattawan ta
amince da sunayen mutane 18 domin a nada su a
matsayin ministoci.
Title :
Korafe-korafe kan wasu ministocin Buhari
Description : Ana ci gaba da samun korafe-korafe a kan wasu daga cikin sunayen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisar dattawa domin nada su...
Rating :
5