A taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC
reshen Sokoto a karkashin shugabancin gwamnan
jihar Aminu Waziri Tambuwal sun ki amincewa
da zabin shugaban kasa akan minista daga jihar.
Taron ya hada da gwamna
mai ci yanzu Tambuwal da tsohon gwamnan jihar
Aliyu Magatakardar Wamako.
A wurin taron jam'iyyar APC ta yi matsaya a
hukumance akan zaben minista daga jihar. Sun ki
amincewa da zabin Shugaban kasa Muhammad
Buhari wanda ya mika sunan Aisha Abubakar
zuwa majalisar dattawa domin a tantance ta ya
nada ta minista.
Gwamnan jihar Sokoto da sauran manyan
jam'iyyar APC da suka halarci taron sun kuduri
aniyar fuskantar shugaban kasa tare da majalisar
dattawa akan maganar domin su gabatar da
matsayin jam'iyyar.
Alhaji Usman Danmadami Isa shi ne shugaban
jam'iyyar APC a jihar Sokoto yace ba zasu goyi
bayan Aisha Abubakar ba. Yace bata san kowa a
jam'iyyar APC a jihar ba. Banda haka karamar
hukuma guda ta fito da gwamnan jihar Aminu
Waziri Tambuwal. Saboda haka babu hujjar da
za'a dauko minista daga yankin.
Amma lamarin na neman haifar da fardiya a
jam'iyyar. Wasu bangarorin suna ma kokarin
ballewa daga jam'iyyar tare da nuna goyon
bayansu da zabin shugaba Buhari.Bangaren shi ne
na rusasshiyar jam'iyyar CPC. Sun yi gangami
akan rashin amincewarsu da matsayin jam'iyyar
APC.
Tsohon shugaban rusasshiyar APC Abubakar Cika
Ainun ya jagorancin bangaren dake barazanar
ballewa da sunan 'yan kasa masu kishi. Yace tare
da Aisha suka yi CPC don haka zargin cewa babu
wanda ya santa ba gaskiya ba ne. Yace tana tare
dasu tun lokacin da suka fara neman wa shugaba
Buhari mulki tun shekarar 2002.
Wasu ma shugabannin jam'iyyar ta APC sun
baranta daga matsayin jam'iyyar akan Aisha
Abubakar.
Duk da badakalar yau Aisha Abubakar zata
bayyana a majalisar dattawa domin tantancewa