Wata Kididdiga da cibiyar bincike kan sha’ainin
abinci ta kasa da kasa ta yi, ta nuna cewa
kasashen masu tasowa guda 52 ne ke fuskantar
barazanar matsananciyar yunwa, kamar yadda
alkaluman da ke nuna matsalar ta yunwa na
Global Hunger Index suka nuna.
Kasar Jamhuriyar Afrika ta
Tsakiya, ita ce tafi kowace kasa fama da
barazanar matsananciyar yunwa a kasashe masu
tasowa bisa alkaluman da aka duba da suka hada
har da matsalar mutuwar yara ‘yan kasa da
shekaru biyar. Sannan sai kasashen Chadi da
kuma Zambia.
Kididdigar ta gano cewa akwai nasaba tsakanin
matsalar yunwa da yake-yake da suka yi fama da
su a shekarun baya, da kuma wadanda suke
aukuwa a yanzu.
Sannan kididdgra ta nuna cewa a sauran jerin
kasashen da ke goman fgarko akwai East Timor,
Saliyo da Haiti Madagascar da Afghanistan da
Nijar da kuma Yemen, wandandu suma duk suna
fusknatr barazanar matsananciyar yunwa.
Dr. Klaus Von Grebmer, mai bincike ne a cibiyar
mai lura da sha’anin abinci a duniya, a Berlin,
inda daga nan ne aka fitar da wannan rahoto.
Kuma a hirar da ya yi da Joe De Capua na sashen
Ingilishi na Muryar Amurka ya danganta matsalar
da rashin zaman lafiya da wasu kasashe ke fama
da su a Afrika.
Yace, “Kasashe biyar cikin takwas na farko daga
Afrika ne, kuma cikin wadannan biyar din hudu
sun tsinci kansu cikin matsananciyar yunwa
saboda yake-yake da a ke yi ko kuma wani abu da
ke da nasaba da tashin hankali.”
Dr Klaus ya kara da cewa- “A duk lokacin da aka
samu tashin hankali na makamai, manoma, ba za
su iya shuka irinsu ba, ko sun shuka ba za a samu
daman sayar da sub a, sannan babu damar shigar
da kayayyakin da za aikin noma da su, baya ga
haka hanyoyin da za a gudanar da kasuwanci duk
sukan kasance a rufe. Saoda haka tasirin da yaki
ke yi akan haifar da yunwa, babban al’amari ne.”
To sai dai a cewar Dr Klaus idan mahukunta suka
himmati, kasashen za su iya saura halin da suka
tsinci kansu a ciki.
“Idan masu rike da mukaman siyasa suka maida
hankali domin ko a nan Afrika, akwai kasashen da
suka yi fama da rikici kuma suka fuskanci wannan
matsala da suka da Habasha da Rwanda da
Angola, amma kuma daga baya da suka samu
zaman lafiya, sai aka maganace matsalar yunwa,
na san akwai wuya, amma za a iya yi.”
Title :
Kasashe 52 Na Fuskantar
Matsananciyar Yunw
Description : Wata Kididdiga da cibiyar bincike kan sha’ainin abinci ta kasa da kasa ta yi, ta nuna cewa kasashen masu tasowa guda 52 ne ke fuskantar b...
Rating :
5