Wani jirgin sojin saman Nigeria mai lamba NAF 801 ya
fadi a karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa arewa
maso gabashin kasar.
Lamarin ya afku ne a yammacin ranar Asabar.
Rahotanni na cewa jirgin ya fado ne a sakamakon
mummmunan yanayi kuma matukin jirgin ne kadai ya ya
rasa ransa a hatsarin.
Rahotanni na cewa babban hafsan sojin saman Nigeriar
ya kafa kwamiti domin gano musabbabin hatsarin jirgin.