Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter yace
yana fatan za'a cimma yarjejeniyar cikin dan
karamin lokaci tsakanin Amurka da Rasha kan
tabbatar lafiyar jirage da matukansu a sararin
samaniyar Syria, domin kaucewa hadari
tsakaninsu.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta
fada jiya Talata cewa a makon jiya jiragen yakin
kasashen biyu sun zo kusa da juna inda kilomita
16 ne kacal suka raba tsakaninsu, har matuka
jiragen suna iya karanta lambobin da aka rubuta
akan jiragen.
Duk da cewa muna ci gaba da jayayya da kan
manufofi gameda Syria, akalla zamu iya cimma
yarjejeniya na tabbatar da lafiyar matuka da
jiragensu" inji Sakatare Carter a wani taro da
manema labarai a Boston jiya Talata. Tilas Rasha
ta gudanar da ayyukanta a sararin Syria da
kwarewa, kuma ta mutunta sharuddan kiyaye
lafiya.
Daga bisani kakakin ma'aikatar tsaron Amurka
Pentagon, Peter Cook, yace jami'an ma'aikatar
zasu tattauna d a takwarorinsu na Rasha ta bidiyo.
Tattaunawar zata fi maida hankali ne kan
sharuddan kiyaye lafiya na matuka jiragen saman
yaki da kayan aikinsu.
Sakatare Carter yace Amurka ba zata canza
shirinta na ci gaba da kai farmaki kan kungiyar
mayakan sakai ta ISIS a Syria b. Duk da haka yayi
kira ga Rasha tayi watsi da shirinta "wanda bashi
da karko", wanda yace ba zai haifi da mai ido ba,
wanda kuma bashi da hangen nesa ko kiyaye abun
da ka faru nan gaba.