Amurka da Rasha dukansu suna kai hare hare
cikin wasu sanssan kasar Syria kowannensu kuma
da tashi manufar da a wani lokacin suna karo da
juna.
Jami’an rundunar sojojin
Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawarsu
karo na uku don fayyace dokoki da ka’idojin
sararin samaniyar Syria.
Domin samin daidaiton fahimtar dokokin salama
wajen aiwatar da ayyukansu da nufin gujewa
hatsarin karon battar da ba a yi niyya ba.
Ma’aikatar tsaron Amurka tace, an sami ci gaba a
taron tattaunawar da ya gudana ta hanyar
sadarwar bidiyo ta yanar gizo a jiya Laraba.
Wanda tattaunawar ta maida hankali ne kacokan a
game da matakan kare lafiya ta wajen kaucewa
arangama.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, taron
ya maida hankali wajen fidda daftarin matsayarsu
a nan gaba.
Dukkan bangarorin kasashen biyu sun yarda da
cewa, an yi tattaunawar bisa kwarewar aiki,
sannan gab ake da cimma yarjejeniya.