Jam’iyyar APC ta bayyana cewa daga tantance tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da majalisa tayi alamun alheri ne da zaya same shi. Majalisar dattawa ta sake dage tantancen Amaechi inda take aka bayyana cewa ana jiran kwamitin dokoki da alfarma su kawo rahotan su akan shi. Anyi tsammanin cewa Yau za’a tantance Shi amma an sake dage tantancewar.
Jam’iyyar APC Ta bayyana Murnar tata ta hanyar shafin ta na Twitter. Suka ce: “Ya kai Amaechi kamar Buhari ma an dage zaben shi. Kai ma zaka yi nasara kamar Mai gidan ka.”
Sannan kuma suka sanya wani bidiyo Inda suke zargin cewa Gwamna Nyesom Wike da kokarin cutar Amaechi. A Yau, 20 ga watan Oktoba ake tsammanin a cigaba da tantance sauran Wadanda suka rage.
Kungiyoyin da yawa sunyi kira da a tantancen Amaechi bisa la’akari da gudunmuwar daya bada.