shugaba Muhammadu Buhari, ya yiwa kasashen
Ingila da Switzerland,godiya dangane da goyon
bayan da suke baiwa Najeriya, na ganin cewa an
dawo da haramtattun kudade
Shugaban kwamitin da
Gwamnatin Najeriya ta Kafa domin bada shawara
wajen magance cin hanci da rashawa a kasar
Farfesa Itsay Sagay, ya ce tun ba ya’u ba akwai
yarjejeniya dake tsakanin kasashe renon Ingila,na
mika duk wani da ake nema a wata kasa na
kungiyar domin fuskantar sharia a wata kasa.
Yace da zaran an samu bukatar na mika wani ko
wata babban lauyan Gwamnati zai gabatar da
wanna bukata ga wata babban kotu, domin
tabbatar da cewa laifin da ake neman wanda ake
zargin da aikatawa ya fada hurumin laifukan da
aka amince a mika mai laifi ga kasar da ta bukaci
hakan.
Ko a wannan makon ma sai da shugaba
Muhammadu Buhari, ya godewa kasashen Ingila
da Switzerland, dangane da goyon bayan da suke
baiwa Najeriya, na ganin cewa an dawo da
haramtattun kudaden da wasu ‘yan siyasa da
shugabani na baya suka sace zuwa kasashen su
abunda kuma ya ce zai taimakawa kasashen wajen
inganta dangantakar tsakanin su.
Bukatar neman mika Deprieye Alamieyeseigha,
tsohon Gwamnan jahar Bayelsa, yaso a dai dai
lokacin da wata tsohowar Minista, a ma’aikatar
man fetur, a zamanin mulkin Jonathan, Diezani
Allison Madueke, ke fuskatar bincike a kasar
Ingila, bisa zargin halarta kudaden haram.